Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Godswill Akpabio ya ce alhakin gwmanati ne dawo da zaman lafiya da haɗin kai a jihar Filato.
Yayin da yake jawabi a taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a jihar yau Asabar a birnin Jos, Akpabio ya ce babu wani daga waje da zai kawo wa ƙasar nan zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Jaridar Dailyu Trust ta rawaito cewa shugaban majalisar dattawan ya yi kira ga ƴan Najeriya su rungumi tsarin zaman lafiya.
Ya kuma jaddada abin da ya kira ƙudurin shugaban ƙasar na magance matsalolin rikice-rikice a faɗin ƙasar.
Yace yaje jihar Plateau ne domin wakiltar shugaban ƙasa, tare da tabbatar da cewa zai yi duk mai yiwuwa domin samar da zaman lafiya.
Yace a duk lokacin da yaji labarin kai hari wata jihar ko wani bangare na Najeriya sai ya zubar da hawaye.
Shugaban majalisar yace rashin zaman lafiya dole ne ya tashi hankalin duk wani dan kishin Ƙasa.

