Dan majalisar dokokin Jihar Kano,mai wakiltar karamar hukumar Gwale Hon.Abdulmajid Isah Umar da akafi Sa ni da Mai Rigar Fata, ya yi zargin cewa wasu mutane daga Abuja da ake turowa cikin majalisar dokokin na ƙoƙarin sayen ‘yan majalisar NNPP domin su koma jam’iyyar APC, lamarin da ya kwatanta da cinikayya irin ta kasuwa.
A cewar dan majalisar, waɗanda suke cikin wannan yunkuri suna bibiyar wasu ‘yan majalisa da tayin kuɗi da wasu alƙawurran siyasa, da nufin rushe ƙarfin jam’iyyarsu ta NNPP tare da ƙarawa APC rinjaye a majalisar.
Saidai Dan majalisar yace wadanda basu da kishin kansu da Akida su ake rinjaya ba iya majalisar dokokin Kano ba har zuwa majalisar Tarayya ta ƙasa.
Ya bayyana hakan ne a cikin wani shiri na musamman da ya halartar a gidan Radiyon Rahma wato GWAMNATI DA JAMA’A wanda gwannatin Kano ke daukar nauyi,Inda yace wannan salon siyasa ba wai kawai yana tauye darajar majalisa ba, har ma yana barazana ga tsarin dimokuraɗiyyar jihar Kano.
“Mun fahimci cewa ana yawo da mu tamkar kayayyakin kasuwa, ana yi mana tayin da dama don mu canja jam’iyya, amma mun ƙi. Mu muna nan a tsaye kan jam’iyyarmu da akidarmu ta Kwankwasiyya saboda amanar jama’ar da suka zaɓe mu,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa duk da matsin lambar da ake ƙoƙarin dora musu, su ba za su karya amanar mazabunsu ba, domin burinsu shi ne ganin sun wakilci al’umma bisa gaskiya da rikon amana.
Dan majalisar ya bayyana lamarin a matsayin wani sabon salo na gurguntar da siyasa da kuma karkatar da hankali daga ainihin ayyukan da ya kamata majalisa ta yi.
Hon.Mai Rigar Fata ya kuma yi tunasar da irin wadannan yan siyasar da su gane cewa kafin zaben shekarar 2023 gwannatin APC ya bari saboda rashin tsari ya dawo jam’iyar NNPP da bata kafa gwannati ba a lokacin.
Daga nan Hon.Mai Rigar Fata ya nemi al’ummar Kano musamman na karkara da su kwantar da hankulansu,kada su yarda a kawo rabuwar kai tsakaninsu da mutanan cikin birni akan ayyukan da gwamna Abba Kabir Yusuf ya ke aiwatarwa,Yana Mai cewa a shekarar 2026 gwamnan ya shiryawa kowanne bangare idan aka duba kasafin kuɗin da zai gabatarwa majalisar da ya tasamma sama da naira Tiliriyan 1

