Hukumar kula da harkokin man fetur a Najeriya (NMDPRA) ta dakatar da shirin karɓar harajin kashi 15 cikin 100 kan man fetur da ake shigo da shi daga ƙasashen waje.
Mai magana da yawun hukumar, George Ene-Ita, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Alhamis, inda ya ce babu buƙatar ‘yan Najeriya su damu kan batun, domin hukumar ta ɗauki matakin ne don sauƙaƙa wa al’umma.
Tun a ranar 29 ga watan Oktoba, Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya amince da kafa wannan haraji kan fetur da dizel, wanda ake sa ran zai ƙara farashin man da ake saukewa a rumbunan rarraba man fetur na Ƙasa wato (depot-depot). Manufar matakin ita ce ƙarfafa matatun mai na cikin gida da rage dogaro da man da ake shigo da shi daga waje.
Gwamnatin tarayya ta tsara fara aiwatar da harajin daga ranar 21 ga watan Nuwamba, kafin hukumar NMDPRA ta sanar da dakatar da shirin.
Masana sun yi gargadin cewa, duk da manufar ƙarfafa matatun cikin gida, aiwatar da harajin na iya jawo hauhawar farashin man fetur a gidajen mai, kasancewar Najeriya na ci gaba da shigo da kaso mai yawa na man da take amfani da shi daga ƙasashen waje.

