Mai ba wa Ministan Babban Birnin Tarayya shawara na musamman kan kafafen sada zumunta, Lere Olayinka, yace sojojin da aka gani suna cacar baka da Nyensom Wike ,hakan ya faru ne sakamakon barazanar harbi da sojojin sukayi a wajen da abinda ya faru.
Rahotanni sun bayyana cewa, rikicin ya faru ne a unguwar Gaduwa da ke Abuja lokacin da jami’an hukumar kula da gine-gine ta FCTA karkashin Nyensom Wike suka je dakatar da wani gini da ake da hukumar tace ba bisa ka’ida ake yi ba.
A cewar Lere Olayinka, sojojin da ke bakin aikin sun hana tawagar ministan shiga wajen, suna masu ikirarin cewa suna aiki ne da umarnin tsohon babban hafsan rundunar sojojin ruwa Vice Admiral Awwal Zubairu Gambo.
Olayinka ya bayyana cewa, sojojin sun yi barazanar harbi ga duk wanda zai kusanci wurin, lamarin da ya fusata Minista Wike, wanda ya bukaci a bar jami’an hukumar ta Abuja su aiwatar da aikinsu kamar yadda doka ta tanada.
TST Hausa ta rawaito cewa a wani bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta, an ga Minista Wike yana muhawara da wani soja da ya hana shi shiga wurin, inda Wike ya jaddada cewa babu wata hukuma ko runduna da ta fi doka karfi a Najeriya.
Mai taimaka wa ministan ya kara da cewa, hukumar FCTA ce kadai ke da hurumin kula da dukkan harkokin kasa da gine-gine a babban birnin tarayya, domin haka duk wani gini da ba ta amince da shi ba, ba bisa ka’ida ba ne.
Sai dai lamarin ya jawo cece-kuce a kafafen yada labarai, yayin da tsohon Minista Osita Chidoka ya bukaci Wike da ya nemi afuwa bisa yadda ya yi wa soja magana da rashin ladabi, yana mai cewa hakan bai dace da matsayin sa a gwamnati ba.
Har yanzu dai babu wata sanarwa ta hukuma daga Rundunar Sojin Najeriya ko hukumar kula da birnin tarayya Abuja kan lamarin, yayin da jama’a ke ci gaba da tattaunawa kan abin da ya faru da kuma yadda aka gudanar da shi.

