A wani rahoto da ƙungiyar Tarayyar Turai (EU) ta fitar ya nuna cewa wani ɓangare na jami’an ‘yan sanda a Najeriya suna mayar da hankali wajen gadin ‘yan siyasa, da attajirai maimakon kare tsaron talakawa wadanda sune mafi rinjaye a Najeriya.
Rahoton ya ce, ƙashi mai yawa daga jami’an ‘yan sanda ( Kashi 1cikin 3 ) na karkatar da ayyukansu wajen kare manyan mutane da masu iko, lamarin da ke rage tasirin su wajen samar da tsaro ga ‘yan ƙasa gaba ɗaya.
Duk da haka, EU ba ta fitar da cikakken rahoton da zai tabbatar da adadin jami’an da abin ya shafa ba.
Saidai TST Hausa ta rawaito cewa masu sharhi sun ce wannan lamari na ƙara haifar da rashin jin daɗin al’umma game da yadda jami’an tsaro ke gudanar da aikinsu.
Hukumomi a bangaren ‘yan sanda sun ce suna kan aiwatar da matakai domin ƙarfafa ayyukan su a fannoni da dama, ciki har da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Sai dai, masana harkokin tsaro sun ja hankalin cewa akwai buƙatar cikakken bincike da ganin ido kafin ɗaukar matakin hukuma ko tabbatar da rahoton.

