Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa gwamnatin sa tana daukar batun samar da wutar lantarki da matuƙar muhimmanci, domin ci gaban Najeriya gaba ɗaya ya ta’allaka ne da samun ingantacciyar wuta.
Tinubu ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karɓi tawagar kamfanin samar da makamashi na Siemens Energy a fadar shugaban ƙasa, inda ya jaddada cewa gwamnati na aiwatar da tsare-tsare na musamman don tabbatar da cewa an inganta samar da wutar lantarki a duk fadin ƙasar.
A cewar shugaban ƙasa, samar da wutar lantarki mai dorewa shi ne ginshiƙin ci gaban masana’antu, ƙarfafa kasuwanci da kuma bunƙasa tattalin arzikin ƙasa.
A wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaban ƙasa Bayo Onanuga,yace Tinubu tunda ya hau Mulkin Najeriya baya daukar samar da Lantarki da wasa.
Ya kuma yaba da haɗin gwiwar da ke tsakanin Najeriya da Siemens wajen aiwatar da shirin samar da makamashi na fadar shugaban ƙasa, wanda ake sa ran zai kawo sauyi a tsarin samar da wutar lantarki a ƙasar.
Add A Comment

