Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta sanar da cewa an soke takardun shiga ƙasar Wato (visa) sama da 80,000 ga ‘yan Najeriya da wasu ƙasashen waje tun farkon wannan shekara.
Wannan mataki na zuwa ne a ƙarƙashin manufofin shugaba Donald Trump, na ƙarfafa tsaro da kiyaye muradun Amurkawa.
Sanarwar ma’aikatar ta bayyana cewa dalilan soke visa ɗin sun haɗa da laifuka daban-daban kamar tuƙi cikin shaye-shaye,da fashi da makami, da sata, da sauran aikata laifuka.
Rahotanni sun nuna cewa kimanin mutane 16,000 aka ci tara kan tuƙi cikin shaye-shaye,sai Kuma mutane 12,000 kan fashi da makami, yayin da 8,000 kan sata.
Bugu da ƙari, ma’aikatar ta ce soke visa ɗin ya haɗa da waɗanda ake zargi da alaka da ayyukan ta’addanci,da goyon baya ga masu tsattsauran ra’ayi, ko kuma wuce wa’adin visa da aka ba su.
Wannan mataki na Amurka na iya shafar ‘yan Najeriya da dama musamman waɗanda ke da shirin tafiya ko zama a ƙasar domin karatu,da aiki, ko yawon shakatawa.
Masu ruwa da tsaki a harkokin shige da fice sun shawarci masu niyyar zuwa Amurka da su kula da bin doka da ƙa’idoji, da tabbatar da sahihancin bayanan da suka bayar wajen neman visa.
Ma’aikatar ta ƙara da cewa matakin soke visa ɗin na ɗaya daga cikin tsauraran matakai na duba cancantar masu shiga ƙasar, kuma yana nufin tabbatar da tsaron duk wanda ke cikin Amurka.

