Limamanin masallacin Juma’a na Usman Bn Affan dake Unguwar Gadon Kaya Karamar hukumar Gwale Dr. Abdallah Usman Gadon Kaya, yayi albishir ga masu fitar da zakka Inda yace su na kasancewa mutane mafi shiga ran jama’a, domin zakka tana tsarkake dukiya,da kuma ƙara imani ga mai ita.
Dr. Abdallah ya bayyana haka ne a yayin gabatar da hudubarsa ta ranar Juma’a, inda ya ce zakka tana da muhimmanci wajen kawo daidaito tsakanin masu hali da marasa hali, da kuma gina zumunci mai ƙarfi a tsakanin al’umma.
A cewarsa, fitar da zakka na nuna godiya ga Allah da amincewa da tsarin adalcin Musulunci.
Ya ce, “Zakka ibada ce da ke goge son kai daga zuciya, tana kuma koya wa mutum jin ƙai da tausayi ga wasu.
“Duk wanda yake fitar da zakka yadda ya kamata, yana nuna cewa yana godewa Allah da ni’imarsa, kuma yana son alheri ga al’umma.”in ji Malamin
Dr. Abdallah Gadon Kaya ya kuma gargadi masu wadata da su guji yin sakaci wajen fitar da zakka, yana mai cewa rashin yin hakan na iya zama sanadin samun matsaloli a rayuwa, domin dukiyar da ba a tsarkake ba tana iya zama fitina ga mai ita.
Ya kuma kafa hujja da ayar Alƙur’ani mai girma inda Allah Maɗaukaki ya ce:
“Khudh min amwâlihim sadaqatan tutahhiruhum wa tuzakkîhim bihâ…”
(Ka karɓi sadaka daga dukiyarsu, domin ta tsarkake su, kuma ta ƙara musu tsarki da ɗaukaka) Suratul Tawbah, aya ta 103.
Dr. Abdallah ya ce wannan aya ta tabbatar da cewa zakka ba wai kawai tana amfanar da marasa hali ba ce, har ma tana tsarkake zuciya da dukiyar mai ita.
Ya ƙara da cewa zakka tana daga cikin ginshiƙan Musulunci da ke tabbatar da adalci, ƙauna da haɗin kai a cikin al’umma, saboda haka ya bukaci musulmi da su riƙa fitar da ita a kan lokaci domin neman yardar Allah da samun albarkar duniya da lahira.
TST Hausa ta rawaito cewa a hudubar Malamin ,ya gargaɗi wadanda ke kallon addinin musulunci a matsayin addinin dake haifar da rikicin musamman kasashen waje,Inda yace babu wani Addini da yafi na Islam son zama lafiya.
Wannan na a matsayin martani ga kalaman Shugaban Amurika Donald Trump dake cewa ana yiwa kiristoci kisan kiyashi ,Inda Dr.Abdallah yace wannan zancen son zuciya ne da neman haddasa fitina.
A karshen Sallar ta Juma’a,Dr.Abdallah Gadon Kaya ya jagoranci adu’ar Alqunuti a raka’ar karshe ta Sallar Juma’ar.

