Hukumar Bunkasa Kimiyyar Halittu ta Ƙasa (NABDA), karkashin jagorancin Farfesa Abdullahi Mustapha ta karrama ɗan jaridar Rahma Radio da RahmaTalabijin Malam Khalid Yusuf Idris, da kyautar gwarzon shekara na ɗaukar rahoto da hoto.
Bikin bayar da kyautar ya gudana ne a dakin taro na Los Angeles Event Center da ke birnin tarayya Abuja, inda aka karrama wasu ‘yan jarida da suka nuna ƙwazo da jajircewa wajen bayar da rahotanni masu alaƙa da harkar noma da kimiyyar halittu.
Da yake jawabi jim kaɗan bayan kammala taron, Shugaban NABDA, Farfesa Abdullahi Mustapha, ya bayyana cewa hukumar tana gudanar da irin wannan karramawa duk shekara, domin yaba wa ‘yan jarida da ke ba da gudunmawa wajen yada ilimi da wayar da kan jama’a, musamman manoma.
TST Hausa ta rawaito cewa Khalid Yusuf Idris ya yi fice wajen jajircewa da kishin al’umma a aikinsa. Yana daga cikin ‘yan jarida da ke ba da lokaci wajen bincike da yada sakonni masu taimakawa manoma wajen habaka amfanin gonarsu. Wannan ne ya sa muka zakulo shi domin girmamawa bisa irin gudunmawar da yake bayarwa wajen ci gaban ƙasa,” in ji Farfesa Mustapha.
A nasa jawabin, Khalid Yusuf Idris ya bayyana farin cikinsa da godiyarsa ga hukumar NABDA bisa wannan karramawa, yana mai cewa lambar za ta ƙara masa ƙwazo da himma wajen ci gaba da gudanar da aikin jarida domin ci gaban al’umma, musamman a fannin noma da kimiyya.
Yace wannan girmamawa hujja ce cewa aikin jarida na gaskiya da sadaukarwa ana ganinsa, kuma wannan zai ƙarfafa ni da sauran ‘yan uwana mu ci gaba da bayar da gudunmawa ga al’umma,” in ji shi.
Bikin ya samu halartar jami’an gwamnati, shugabannin cibiyoyi, da wakilan ƙungiyoyin ‘yan jarida daga sassa daban-daban na ƙasar.

