Gwamnatin Kasar China ta bayyana goyon bayanta ga gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu, tana mai jaddada cewa tana tare da Najeriya a ƙoƙarinta na cimma ci gaba mai ɗorewa bisa yanayin ƙasar.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen China, Mao Ning, ce ta bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a ranar Talata.
A cewarta, “A matsayinta na abokiyar hulɗa ta dabarun ci gaba da Najeriya, China tana adawa da duk wata ƙasa da ke amfani da addini ko kare haƙƙin ɗan adam a matsayin hujja don tsoma baki cikin harkokin wasu ƙasashe, ko kuma yin barazanar takunkumi da amfani da ƙarfi.”
Mao Ning ta bayyana hakan ne yayin da take amsa tambaya kan barazanar da Shugaban Ƙasar Amurka, Donald Trump, ya yi na kai hari a Najeriya bisa zargin cin zarafin Kiristoci.
Ta ƙara da cewa, China tana da tabbacin cewa gwamnatin Najeriya ƙarƙashin shugabancin Bola Tinubu za ta ci gaba da tafiya a kan tafarkin zaman lafiya, ci gaba da mutunta ‘yancin jama’a, da kuma kare ‘yancin ƙasar daga duk wata tsoma bakin ƙasashen waje.

