Shugaban Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Najeriya Human right network of Nigeria kuma Shahararren mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, Kwamared A.A Haruna Ayagi, ya caccaki ‘yan majalisun dokokin jihohin Najeriya, yana masu zargi da zama ‘yan amshin shata ga gwamnoninsu, maimakon kare muradun jama’ar da suka zabe su.
Ayagi ya bayyana haka ne a cikin wani shiri na musamman a gidan Radiyon Rahma dake Kano,inda ya bayyana cewa mafi yawan yan majalisun dokoki na jihohi sun gaza sauke nauyin da aka dora musu na sa ido kan ayyukan gwamnoni da kare maslahar jama’a.
A cewarsa, ‘yan majalisa da dama sun koma masu amincewa da duk wani kuduri ko shawarar da gwamna ya kawo, ba tare da bincike ko tsayuwar daka ba.
“Yawancin yan majalisun dokoki a jihohin Najeriya sun zama ‘yan amshin shata duk da nasan basa son sunan nan,Amma dole mu fada ,tunda su ma ba sa kare muradin al’umma, sai dai su yi abin da gwamna ya ce. Wannan halin yana lalata dimokuraɗiyya a ƙasar,” in ji Ayagi.
Ya kuma bukaci ‘yan majalisa su tuna cewa jama’a ne suka zabe su don kare hakkinsu, ba don su zama masu bin umarnin gwamnoni ba.
Ayagi ya ce lokaci ya yi da za a farka daga wannan sakaci domin mayar da majalisu cibiyoyi masu zaman kansu da ke iya tsayawa da gaskiya wajen tafiyar da mulkin dimokuraɗiyya a Najeriya.

