Shugaban sashen ilimin Ƙasa na jami’ar Northwest dake Kano Dr.Nazifi Umar Alaramma ya ce abu ne mai kyau gwamnatin tarayya ta dawo da darasin ilimin Ƙasa cikin manhajar koyar da dalibai a makarantun sakandire ya zama tilas maimakon zabi saboda mahimmacinsa.
A shekarar 2013 ne gwannatin tarayya ta cire darasin ilimin Geography a matsayin dole ga ɗaliban sakandare Inda ya koma a matsayin zabi ga daliban.
Saidai kuma Dr.Nazifi Umar Alaramma yace da yiyuwar a babban taron Kungiyar masana ilimin Ƙasa na Najeriya wato Association of Nigerian Geographers ANG da jami’ar Northwest zata karbi bakuncinsa a shekarar 2025 za’a tattauna batun neman dawo da wajabta ilimin Geography a matsayin wajibi ga dalibai.
Taron karo na 65 zai karbi manyan baki da masana ilimin Ƙasa daga jihohin Najeriya da dama domin baje basirarsu.
Zan kuma a tattauna mahimman batutuwa da suka shafi cigaban kasashen duniya musamman masu tasowa.
Dr.Nazifi Umar ya shaida hakan ne a taron manema labarai gabanin taron na Kungiyar masana ilimin Ƙasa da za’ayi a Kano daga ranar 5 ga watan Oktoba zuwa 9.
Taken taron na ANG na bana shi ne :
“Binciken raunin yanayi,da bambancin tattalin arziki da rashin daidaito a cikin al’umma a kasashe masu tasowa.”
A yayin taron na manema labarai Dr.Nazifi Alaramma wanda shine mai shirya wajen zama yace Kamar yadda aka dawo da wajabawa daliban sakandire koyon darasin ilimin Tarihi wato History a Najeriya ya Bayan kamata gwannatin tarayya ta dauki irin wannan matakin ga Geography.
Dr. Nazifi Umar Alaramma, ya yi kira ga gwamnati da masu tsara manufofin ilimi da su dawo da darasin Geography a matsayin darasi dole ga ɗalibai.
Yace akwai fatan cewa masana da masu ruwa da tsaki zasu gabatar da wannan bukata a yayin taron da za’a gudanar a Jami’ar Northwest a Kano.
A cewarsa, Geography darasi ne da yake da muhimmanci wajen fahimtar yadda duniya ke tafiya, da dangantakar mutum da muhalli, da kuma matsalolin da ke shafar rayuwar yau da kullum, irin su dumamar yanayi, rarrabuwar albarkatu da ƙauracewar jama’a daga wuri zuwa wuri.
Dr. Nazifi ya bayyana cewa cire darasin daga matsayin dole ya rage sanin ɗalibai a fannin da ke da alaƙa da tsare-tsaren ci gaban ƙasa.
“Kamar yadda aka fahimci muhimmancin Tarihi har aka dawo da shi, haka ya kamata a fahimci muhimmancin Geography, domin ya na da tasiri wajen haɓaka tunanin matasa da kuma samar da ƙwararru a fannoni irin su tsara birane, da aikin noma, kula da muhalli da binciken ƙasa,” inji shi.
TST Hausa ta rawaito cewa a kalla masana 250 ne zasu gabatar da mukala a wajen taron na bana

