Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya kaddamar da biyan tsofaffin kansiloli haƙƙoƙinsu karo na biyu, domin tabbatar da adalci da cika alkawarin gwamnatinsa na kula da waɗanda suka yi wa jihar hidima a baya.
Tsaffin kansilolin sunyi aiki ne da tsohon gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje a tsakanin shekarar 2018 zuwa 2020.
TST Hausa ta rawaito cewa kuɗaden sun tasamma sama da naira miliyan dubu 5 da miliyan dari 6.
A yayin taron kaddamarwar, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa gwamnatin Kano za ta ci gaba da ɗaukar matakan tallafa wa tsofaffin kansilolin da suka yi aiki da gwamnatin baya harda tsaffin shugabannin ƙananan hukumomi da suka yi hidima, tare da tabbatar da cewa kowa ya samu abin da ya dace da shi.
Ya kuma jaddada cewa gwamnatinsa na aiwatar da manufofi da suka shafi walwalar jama’a da tabbatar da gaskiya da adalci a cikin dukkanin al’amuran gwamnati.
A nasu jawabin, wasu daga cikin tsofaffin kansilolin da suka halarci taron sun bayyana jin daɗinsu kan wannan mataki, inda suka yaba da yadda gwamnan ke cika alkawuransa tare da nuna kulawa ga masu ruwa da tsaki a fagen siyasa da mulki.
TST Hausa ta rawaito cewa a karshen watan Afirilun shekarar 2025 ne gwamna Yusuf ya amince da sakin naira miliyan dubu 15 da miliyan dari 6 domin biyan hakkokin tsaffin kansilolin su sama da dubu 3 wadanda sukayi aiki daga shekarar 2014 zuwa 2017 da 2018 zuwa 2020 sai Kuma 2021 zuwa 2024.

