Kwalejin Koyar da Aikin Gona ta Audu Bako da ke karamar hukumar Dambatta ta musanta zargin kin bin umarnin gwamnatin jihar Kano.
Shugaban makarantar, Farfesa Muhammad Audu Wailare, ya bayyana haka a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a ofishinsa.
Farfesa Wailare ya ce shugaban kungiyar malaman kwalejojin kimiyya da fasaha ta kasa (ASUP) reshen Arewa maso Yamma, Dakta Abdulaziz Badaru, na yada bayanai marasa tushe kan dakatar da wani malami, Ahmad, bisa zargin duka da ya yi wa abokin aikinsa a bainar jama’a.
Ya bayyana cewa hukuncin ya biyo bayan binciken da makarantar tare da hukumar ma’aikatan jihar suka gudanar, inda aka cimma matsayar dakatar da malamin, ba wai kin bin umarnin gwamnati ba.
Shugaban kwalejin ya kuma zargi Dakta Badaru da amfani da kafafen yada labarai wajen bata sunan makarantar, tare da ikirarin cewa ta bijirewa gwamnatin jihar Kano.
A cewarsa, a tsawon shekarun da yake rike da shugabancin makarantar, babu wata gwamnati da ta baiwa kwalejin kulawa da muhimmanci kamar gwamnatin mai girma Gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf.

