Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya kaddamar da rabon kashi na farko na shirin tallafa wa matasa domin su dogara da kansu ko kara jari kasuwancinsu.
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Hon.Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar,yace shirin ya bai wa matasa 5,384 maza da mata damar samun tallafin Naira 150,000 kowannensu, wanda ya kai jimillar Naira 807,000,000.
A yayin kaddamar da shirin, Gwamna Yusuf ya ce an tsara wannan mataki ne domin ba matasa damar shiga harkokin kasuwanci yadda ya kamata tare da bayar da gudummawa wajen ci gaban al’umma.
Ya bukaci wadanda suka amfana da tallafin da su yi amfani da shi ta hanyar da ta dace, domin inganta harkokinsu da kuma samar musu da makoma mai kyau.
Gwamnan ya kuma roki wadanda ke cikin jerin jiran rabon su da su yi hakuri, inda ya tabbatar musu da cewa kashi na biyu na shirin zai biyo baya nan ba da jimawa ba.
Ya kara jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da bai wa shirye-shiryen da suka shafi matasa da samar musu hanyoyin dogaro da kai muhimmanci a fadin Jihar Kano.

