Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya ce alkawarin da gwamnatinsa ta ɗauka na kare dukiyoyin al’ummar jihar ne ya sa jama’a suka ba shi amana a zaɓen shekarar 2023.
A cewarsa, gwamnati na mayar da hankali wajen tabbatar da amanar da aka ɗora mata, ta hanyar sarrafa kuɗaɗen shiga da ake samu daga tara haraji domin inganta rayuwar jama’a.
Gwamna Yusuf ya shaida hakan ne a Kaduna yayin rufe taron kwanaki uku kan sanin makamar aiki da aka shiryawa jami’an gwamnatin Kano.
“Manufar taron shi ne yaki da cin hanci da rashawa,da magance zurarewar kuɗaden gwamnati da samar da Shugabanci na gari da kuma nuna ƙwarewar aiki da bin dokokin aikin”
Gwamna Yusuf ya shaidawa mahalarta taron cewa gwamnatinsa ta yi duk mai yiyuwa wajen magance zurarewar kuɗaden gwamnati da kuma yaki da cin hanci da rashawa.
“Muna samun manyan kuɗaɗe ta hanyar tara haraji, kuma muna amfani da kuɗaden wajen samar da kayan more rayuwa, kamar tituna, fitulun kan hanya, da inganta ilimi da lafiya,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa manufar gwamnati shi ne tabbatar da cewa kowanne ɗan Kano ya amfana da kuɗaɗen da ake tarawa, ta hanyar gudanar da ayyuka masu tasiri ga ci gaban al’umma.
TST Hausa ta rawaito cewa taron ya hada da kwamshinonin Kano da masu baiwa gwamna shawara da mataimakansa na musamman da manyan sakatarorin gwamnati da sauran jami’an gwamnatin da dama.
A karshen Jawabinsa , gwamna Yusuf ya nemi jami’an gwamnatin da suka kammala karɓar wannan horo na sanin makamar aiki da suyi amfani da abinda suka koya a Jihar ta Kaduna.

