Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa gwamnatin sa ta kuduri aniyar kammala biyan hakkokin ’yan fansho kafin shekarar 2027.
Gwamnan ya ce an shafe shekaru ana tarawa ’yan fansho basussuka a jihar, abin da ya jefa dubban tsofaffin ma’aikata cikin mawuyacin hali, amma gwamnatinsa ta dauki matakin shawo kan matsalar cikin gaggawa.
Gwamnan na wannan jawabin ne a dakin taro na gidan gwamnatin jiha, lokacin kaddamar da biyan hakkokin yan Fansho naira biliyan 5 karo na biyar.
Gwamna Yusuf yace ba za’a tashi daga taron ba ,har sai kowanne dan fansho yaga kuɗinsa a wayarsa ta salula.
A cewarsa, gwamnatin Kano ta riga ta tsara hanyoyi na musamman da za su tabbatar da cewa ba a sake jinkirta biyan hakkokin wadanda suka yi wa jihar hidima ba.
“Mun yi imani cewa wanda ya yi wa jihar aiki ya cancanci samun hakkinsa ba tare da wahala ba”In ji gwamna Yusuf.
“Saboda haka kafin karshen wa’adinmu a 2027, babu wani mai fansho da zai rage da korafi a Kano,” in ji Gwamna Yusuf.
Ya kara da cewa, gwamnatin sa za ta ci gaba da hada kai da kungiyoyin ’yan fansho da sauran masu ruwa da tsaki don tabbatar da gaskiya da adalci a tsarin biyan fansho.
Kafin hawansa mulki, gwamna Yusuf yace an bar masa bashin yan Fansho sama da naira biliyan 48.
Zuwa yanzu an warware bashin da ya kai naira biliyan 27

