Babban bankin musulunci a Najeriya Jaiz Bank ya samu lambar yabo ta bankin da yafi ko wanne banki cigaba a Najeriya a shekarar 2025 wato Most Progressive Islamic Bank 2025 saboda irin ci gaban da ya samu a harkokin banki bisa tsarin Musulunci.
Bankin shi ne kan gaba wajen kyautatawa yan Najeriya.
An ba da wannan lambar yabo ne a wani taron kasa da kasa da ke karrama cibiyoyin kudi da suke taka rawa wajen inganta ayyukan banki bisa ka’idojin shari’ar Musulunci.
A cikin jawabin bankin, Jaiz Bank ya bayyana cewa wannan nasara alama ce ta amincewa da jajircewar da ya yi wajen samar da sabbin hanyoyi da sauƙaƙa wa al’umma samun ayyukan banki na zamani cikin halal.
Bankin ya kuma yaba da goyon bayan abokan huldarsa da al’umma, yana mai tabbatar da cewa zai ci gaba da bunkasa ayyukansa domin tallafawa tattalin arzikin kasa da kuma tabbatar da ci gaban harkar bankin Musulunci a Najeriya.
Bankin Jaiz Bank Plc shi ne bankin Musulunci na farko a Najeriya.
An fara bude shi a hukumance a ranar 6 ga Janairu, 2012, bayan samun lasisi daga Babban Bankin Najeriya (CBN).
TST Hausa ta rawaito cewa an bude bankin ne a zamanin shugabanincin tsohon gwamnan bankin Sunusi Lamido Sunusi

