Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da mika dokar haramta auren jinsi a Kano zuwa majalisar dokokin Kano domin ta zama doka ta shekarar 2024.
Gwamna Yusuf ya amince da hakan ne bayan kammala taron majalisar zartaswa ta jihar Kano karo na 31 da aka gudanar a masaukin gwamnatin jiha dake rukunin gidajen birnin Kwankwansiyya.
A cikin abubuwan da majalisar zartaswar ta amince da haramcinsu,bayan auren jinsi a Kano harda Madugo da Luwadi wanda duka gwamnatin Kano tace haramun ne aikata su a jihar.
Sannan majalisar ta amince a tura dokar baiwa kananan hukumomin kano yancin gashin kansu domin itama ta zama doka.
TST Hausa ta rawaito cewa a yayin kammala zaman majalisar zartaswar,an amince da Kashe kuɗi sama da naira miliyan dubu 18 da miliyan dari 8 domin gudanar da manya da kananan ayyuka 35 a ciki da wajen birnin Kano.
Ayyukan sun hada da gyaran makarantun Furamare da sakandire,da samar da ruwan sha da fitulun kan hanya masu amfani da hasken rana,da gyara tituna da gyara motocin kwashe shara .
A yayinda yake karin haske kan abinda majalisar zartaswar ta amince da su, kwamishinan kasa da Safiyo na Jihar Kano Abduljabbar Umar Garko yace an amince da samar da magudanan ruwa a Unguwannin Kofar Wambai da Zage da sauran Unguwannin birnin Kano.
Kwamishinan yace duka ayyukan sun shafi cigaban jama’ar Kano a bangarori da dama,kai tsaye musamman koshin lafiya da Ilimi da cigaban matasa da mata da kayan more rayuwa.

