Gwamnatin Kano ta yi barazanar rufe duk wata makaranta mai zaman kanta da ta kara kuɗin makaranta ga Iyayen yara ba bisa ka’ida ba.
Shugaban Hukumar kula da makarantu masu zaman kansu ta jihar Kano Baba Abubakar Umar , ya yi wannan gargaɗin a ranar Al-hamis din nan yayin da yake ganawa da manema labarai a Kano.
Yace duk makarantar da aka samu da laifi za’a gurfanar da ita gaban kotu bayan rufe makarantar.
Baba Abubakar Tarauni, ya ce Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ya dauki wannan matakin ne sakamakon koke koken da iyayen yara ke yi na karin kudin da makarantun da tsauwalawa wajen siyan littafai da kayan makaranta.
Sannan shugaban ya ce, za su fara rufe makarantun da ke biyan masu kwalin Digiri kasa da Dubu 20 da kuma masu tilasta biyan kudin biki.
Sannan shugaban hukumar Baba Abubakar Tarauni ya ce, ya bukaci iyaye da su dinga biyan kudin makaranta akan lokaci.
TST Hausa ta rawaito cewa shugaban hukumar ya bukaci iyaye da su dinga biyan kudin makaranta akan lokaci.
A kwanan nan da aka koma makaranta, iyayen yara a Kano sun koka da karin kuɗin makaranta da kuɗin littatafai da ake tursas musu saya ba bisa ka’ida ba.

