Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya ce baya ƙarƙashin Iko ko abin koyi a siyasance daga wajen tsohon gwamnan jihar, Malam Nasir El-Rufai Ina ya jaddada cewa manyan jagororin da suka haskaka masa hanyar siyasa su ne Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu da marigayi lauya mai rajin kare haƙƙin ɗan Adam, Cif Gani Fawehinmi.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa,da aka yi dashi inda ya ce tun a shekarar 1994 ya fara haɗuwa da Tinubu a gidan marigayi Beko Ransome-Kuti, sannan kuma ya rayu a gidan Gani Fawehinmi lokacin gwagwarmayar kare dimokuraɗiyya a ƙasa.
Uba Sani ya ce manufarsa ita ce gudanar da mulki yadda ya dace domin amfanin al’umma, ba wai dogaro da mutum ko neman tallafi daga wani tsohon shugaba ba.
Haka kuma, ya karyata zargin da ake yi wa gwamnatin sa na biyan kudin fansa ga ‘yan bindiga musamman a yankin Birnin Gwari.
Ya kara dacewa dabarun tsaro da ake amfani da su a wannan yanki sun fi karkata ne ga haɗin guiwar al’umma da hanyoyin zaman lafiya, ba wai biyan kudin fansa ba.
Gwamnan ya ja hankalin al’umma da su yi watsi da irin waɗannan jita-jita, yana mai cewa wasu ‘yan siyasa ne kawai ke yada su don neman mabambanta ra’ayi da kawo cikas ga gwamnatin sa.
Ya nemi yan Kaduna da su daina kallon tsohon gwamnan jihar Nasiru El-rufai a matsayin uban gidansa na siyasa.

