Wasu daga cikin jiga-jigan jam’iyyar NNPP a Kano sun bayyana cewa sun kori dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Kiru da Bebeji Hon Abdulmunin Jibiril Kofa ne saboda zargin ƙoƙarin cefanar da ’yancin jagoran jam’iyyar NNPP na kasa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, a wajen Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu.
Hon. Alhajiji Nagoda wanda shine mai taimakawa gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf a bangaren yada labarai shine ya bayyana hakan a hirarsa da TST Hausa a ranar Lahadi.
A cewarsa wannan mataki da dan majalisar Kofa ke kokarin dauka ya saba da muradun jam’iyyar NNPP da kuma tsarin tafiyar Kwankwasiyya, a dan haka suka ɗauki matakin nesanta kansu da Kofa din domin kare mutuncin jam’iyya da kuma ci gaban siyasar su.
Hon.Nagoda yace duk ziyarar da Kofa ke kaiwa Tinubu,yana yi ne bisa radin kansa ,kuma sun gano yana neman haddasa rikicin siyasa tsakanin Kwankwaso da Tinubu.
“Burin Kofa na neman hada rikicin siyasa tsakanin Tinubu da Kwankwaso bai cika ba muka gano shi” ,In ji Hon Nagoda.
A halin yanzu, Nagoda yace duk mutumin da ba zai kawo cigaba a tafiyar Kwankwasiyya ba rabuwa dashi yafi zama daidai a siyasance.
Mai taimakawa gwamnan na Kano Hon Alhajiji Nagoda yace magoya bayan Kwankwasiyya na tare da hukuncin da aka ɗauka, na korar Kofa daga jam’iyyar NNPP.
Daga karshe Nagoda yace akwai kyakkyawar fahimtar juna tsakanin Tinubu da Kwankwaso,kuma mutane biyun suna girmama juna.

