Tsohon shugaban kasa, Dr. Goodluck Ebele Jonathan, ya koka da yadda ya ce siyasar Najeriya ta kunshi abubuwa da dama na cin amana da rashin tsayawa a kan alkawari da gaskiya.
Ya kuma koka dacewa anci amanarsa a lokacin da yake neman wa’adi na biyu a zaben shugaban kasa na shekarar 2015, wanda ya kai ga faduwar sa a hannun Shugaba Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC.
Jonathan ya bayyana hakan ne a lokacin bikin zagayowar cika shekara 70 da haihuwar tsohon Shugaban ma’aikatansa, Cif Mike Aiyegbeni Oghiadomhe, a birnin Benin, jihar Edo.
Ya ce a siyasar Najeriya, cin amana ya yi yawa.
Jonathan ya yi nuni da cewa irin wannan dabi’a ta sa ya fuskanci matsaloli da suka kawo cikas ga burinsa na komawa mulki a karo na biyu.
TST Hausa ta rawaito cewa a gabanin zaɓen 2015 ,mukarraban gwamnatin Jonathan sun ta ficewa daga PDP suna komawa jam’iyyar hadaka ta APC a lokacin.
Duk da haka, ya yabawa tsohon shugaban ma’aikata na zamanin nasa Oghiadomhe saboda jajircewarsa da amincinsa a lokacin da ya fi bukatar goyon baya.
Jonathan ya kara jaddada cewa irin wadannan mutane masu gaskiya da amana ba su da yawa a fagen siyasar Najeriya, inda yawanci abin ya ta’allaka ne da canza sheka da kuma cin moriyar kai.
Tsohon shugaban ya kammala da kira ga ‘yan siyasa su rinka tsayawa kan gaskiya da alkawarin da suka dauka, domin ceto martabar dimokuradiyya a Najeriya.

