Gwamnatin Tarayya amadadin Shugaban kasa Bola Tinubu ta karrama ɗalibar nan Arewacin Najeriya Nafisah Abdullahi, wadda ta lashe gasar ƙarshe ta TeenEagle Global Finals Competition, ta duniya inda ta samu kyautar kuɗi naira dubu dari biyu (₦200,000).
Ministan Ilimi na Najeriya Dr. Tunji Alausa ya mika kyautar kuɗin a ma’aikatar Ilimi a wani biki na musamman da aka shirya domin karram ɗalibar da sauran daliban da sukayi Nasara.
TST Hausa ta rawaito cewa a baya bayan nan yan Najeriya musamman daga Arewa sun ta kiraye kirayen a tallafawa ɗalibar da kuma karrama ta saboda bajintar da tayi.
Nafisah Abdullahi ta samu nasarar ne bayan ta fafata da ɗalibai daga sassa daban-daban na duniya a fannin harshen Turanci, inda ta nuna bajintarta ta hanyar rubutu, magana da fahimtar nahawu.
Wannan ya sa ta zama wakiliyyar Najeriya ta farko da ta ɗauki kambun gasar a wannan mataki, abin da ya sanya ƙasar ta yi alfahari da ita.
Da yake gabatar da kyautar, jami’in gwamnatin tarayya ya bayyana cewa, wannan karramawa na nufin karfafa gwiwar sauran matasa su ma su dukufa wajen neman ilimi da kuma kawo wa Najeriya suna a duniya.
“Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da tallafawa matasa masu basira a fannoni daban-daban domin ganin sun zama gatan ƙasa a nan gaba,” in ji shi.
A nata jawabin, Nafisah Abdullahi ta nuna farin cikin ta, inda ta ce nasarar ba ta kanta ba ce kawai, amma ta dukkan matasan Najeriya.
Ta kuma gode wa iyayenta, malamanta da gwamnatin da ta yi mata wannan kyauta.
Masu lura da al’amura sun bayyana cewa irin wannan karramawa na da muhimmanci wajen ƙarfafa matasa da kuma nuna muhimmancin karatu da ƙwazo wajen cimma nasara.

