DAUKAR NAUYI:Magoya bayan kauran Bauchi
Wata kungiyar cigaban matasan Najeriya wato Nigerian Youth Progressive Forum (NYPF), karkashin jagorancin shugaban ta na ƙasa, Alhaji Nura Bala Kuta (Yariman Ƙauran Bauchi), ta bukaci gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad (Ƙauran Bauchi), da ya tsaya takarar shugabancin Najeriya a babban zaben 2027.
Wannan kira ya fito ne yayin taron matasa masu magoya bayan Sanata Bala Muhammad da kungiyar ta shirya a dakin taro na Mumbayya House, da ke Kano, wanda ya samu halartar manyan ‘yan siyasa daga sassa daban-daban na ciki da wajen jihar.
A jawabinsa, Alhaji Nura Bala Kuta ya bayyana cewa, Sanata Bala Muhammad ya fi dacewa da shugabancin ƙasa, duba da irin gagarumin ayyukan ci gaban da ya gudanar a Jihar Bauchi da kuma lokacin da yake Ministan Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Ya ce, “Kaura ne kaɗai zai iya ceto Najeriya daga halin matsanancin rashin tsaro da we durƙushewar tattalin arziki da ake fama da shi a halin yanzu”
Sun nemi gwamnan da kada ya tula musu kasa a Ido.
Gwamnan na Bauchi ya fara mulkin jihar ne tun a shekarar 2019 a jam’iyar PDP kuma wa’adin mulkinsa zai kare ne a shekarar 2027.

