Gwamnatin jihar Kano ta bukaci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da ta samar da karin rumfuman zabe a mazabun jihar Kano 484 domin rage cunkoson da ake fuskanta a lokacin zabe.
Shugaban kwamitin wayar da kan al’uma kan muhimmancin mallakar katin zabe kuma kwamishinan yada labarai Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya bukaci haka yayin kwamitin ya ziyarci shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa reshen jihar Kano Ambassada Abdu Zango a ofishinsa.
Kwamared Waiya ya ce an samu karin sabbin gundumomi da unguwanni a jihar Kano wadanda suke bukar a shigar dasu cikin jadawalin hukumar, inda ya kuma bukaci a rage alkaluman rumfuman da ake samun cunkoso zuwa sabbin rumfuman zaben da za a kirkira.
Ya ce a shirye kwamitin yake ya yi kafada-da-kafada da hukumar domin wayar da kan al’umma tare da taimaka musu ta kowace fuska.
A nasa bangaren shugaban Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa reshen jihar Kano Ambassada Abdu Zango ya ce akwai sama da katin zabe 360,000 da har yanzu masu su basu zo sun karɓa ba a jihar Kano.
Don haka ya bukaci kwamitin da ya wayar da kan waɗanda suka yi rijista su zo ofishin hukumar domin karbar katinsu.
A yayin ziyarar, shugaban kwamitin na tare da wakilai da sakatarorin kwamitin.

