DAUKAR NAUYI :Magoya bayan Shehu Isa Direba a Tarauni
Wani dan siyasa kuma jigo a jam’iyyar APC,a Kano Hon. Shehu Isah Driver, ya ce al’ummar jihar sun fara ganin irin gagarumin tasirin da mataimakin Shugaban majalisar dattawa ta Najeriya Sanata Barau I. Jibrin yake da shi a siyasar jihar da ma kasa baki ɗaya.
A cewar Driver, a yanzu duk wani ɗan APC a Kano ya zama wajibi ya kalli Sanata Barau a matsayin jagora kuma mutum mai daraja a jam’iyyar.
Ya ce rawar da Barau yake takawa wajen tabbatar da martabar jam’iyyar a Kano ta sa ya cancanci a girmama shi a duk wani mataki.
“Yanzu mazauna Kano, ko da kuwa ‘yan adawa ne, sun fahimci wanene Sanata Barau, wannan ne ya sa kowanne ɗan APC ya rusuna ya yaba da irin jagorancin sa, domin ya nuna kishin jihar da jam’iyya, idan aka kalli rawar da ya taka a zaben cike gibi na dan majalisar jiha a Tsanyawa da Ghari harma da Shanono da Bagwai” in ji Driver.
Hon. Driver ya kuma yi nuni da cewa a mazabun Shanono da Bagwai, inda jam’iyyar NNPP da Kwankwasiyya suka daɗe suna da rinjaye, an fara ganin alamun sauyi.
Ya bayyana cewa jama’a a yankunan sun fara gane cewa siyasar Kano tana karkata ne zuwa ga irin tasirin da Sanata Barau ke da shi.
Driver ya ƙara da cewa Sanata Barau ya tabbatar da cewa ba kawai wakilcin majalisar dattawa yake kansa ba, har ma ya zama jigo na haɗa kan jama’a da tabbatar da ci gaban Kano.
Ya kuma yi kira ga dukkan yayan jam’iyyar APC a Kano da su rungumi haɗin kai tare da mara baya ga Sanatan, domin a cewarsa hakan shi ne hanya mafi dacewa wajen tabbatar da nasarar jam’iyyar a nan gaba.
TST Hausa ta gano cewa watakila kalaman na Shehu Isa Direba wanda ya kasance tsohon mai baiwa tsohon gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje shawara akan harkokin yada Labarai su tada kura a siyasar APCn Kano ganin cewa an samu rabuwar kai game da jagorancin jami’yyar da rawar da kowanne bangare ke takawa.

