Kungiyar al’umar Musulmin jihar Lagos wato Community of Lagos State (MCLS) ta bayyana aniyar ta na janye goyon baya ga duk wata jam’iyyar siyasa da ba ta tsayar da dan takarar gwamna Musulmi ba a zaben gwamnan jihar Lagos na shekarar 2027.
Kungiyar a madadin Musulmin Lagos ta bayyana wannan matsaya ne a yayin babban taron kungiyar da aka gudanar a Masallacin Sakatariyar kungiyar dake yankin Alausa a Jihar.
KARIN LABARAI :https://tsthausa.com/duk-wani-dan-arewa-da-yasan-ciwon-kansa-ba-zai-goyi-bayan-apc-a-zaben-2027-ba-inji-pdp/
Mahalarta taron sun bayyana damuwarsu kan abin da suka kira keɓe Musulmai daga muhimman mukamai a shugabanci, musamman a bangaren ilimi.
Taron ya bukaci Gwamnatin Jihar Lagos da ta dauki ƙarin malamai na Larabci da Ilimin Addinin Musulunci a makarantun gwamnati, tare da tabbatar da adalci da daidaiton addini wajen nada shugabanni a matakai daban daban.
Kungiyar ta ce ta dauki wannan mataki ne sakamakon abin da ta bayyana a matsayin rashin isasshen wakilcin Musulmai a manyan mukaman siyasa da na gwamnati a jihar, duk da cewa Musulmai na daga cikin mafi rinjayen al’ummar Lagos.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/duk-%c9%97an-fanshon-da-bai-za%c9%93i-abba-yusuf-a-2027-ba-ya-ci-amanarmu-nup/
A cewar kungiyar tsawon shekaru 12 ana mulkin jihar Lagos karkashin gwamnonin Kirista, ciki harda na yanzu lamarin da kungiyar ke ganin ya dace a sauya domin a samu daidaito, adalci da wakilci ga kowane bangare na al’umma.
Kungiyar ta yi kira ga jam’iyyun siyasa da su mutunta muradin al’ummar Musulmi, tare da jaddada cewa duk jam’iyyar da ta bijire wa wannan bukata, za ta rasa kuri’un Musulmai a zaben 2027.
Haka kuma,kungiyar ta bukaci Musulmai da su kara shiga harkokin siyasa,sannan su je su yi rijistar katin zabe, su kuma fito kwansu da kwarkwatarsu wajen mara wa ‘yan takarar Musulmi baya.
Daga cikin batutuwan da aka tattauna a taron akwai bukatar inganta koyar da harshen Larabci da ilimin Addinin Musulunci a makarantun jihar, da kuma kira ga gwamnatin Lagos da ta mutunta hukuncin Kotun Koli kan sanya hijabi ga daliban mata Musulmi.
Masu sharhi kan al’amuran siyasa na ganin wannan matsaya ta Musulman Lagos na iya tasiri sosai wajen tsara dabaru da tsayar da ‘yan takara da jam’iyyun siyasa za su yi gabanin zaben gwamna na shekarar 2027.

