Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa shigar ɗansa, Abba Abubakar, cikin jam’iyyar APC shawara ce ta kansa yana mai jaddada cewa wannan ya nuna yancin da yake da shi a Demokaradiya.
Atiku ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya Wallafa a shafinsa na Facebook , inda ya ce a tsarin dimokuraɗiyya, ’yancin zaɓi da lamirin mutum su ne ginshiƙan siyasa, kuma hakan ba ya gushewa ko da siyasa da alakar iyali sun haɗu.
Ya ƙara da cewa, a matsayinsa na mai kishin dimokuraɗiyya, ba ya tilasta wa ’ya’yansa ra’ayi ko matsaya kan abin da ya shafi lamiri, kuma ba zai taɓa tilasta wa ’yan Najeriya irin wannan ba.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/2027kafin-mako-biyuatiku-da-peter-da-el-rufai-da-suka-amince-adc-ce-zata-kada-apc-zasu-kammala-ganawa-inji-adc/
Sai dai tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa ya bayyana damuwa mai tsanani kan abin da ya kira gazawar shugabancin jam’iyyar APC, yana mai zargin jam’iyyar da haddasa matsanancin ƙalubalen tattalin arziki da zamantakewa a ƙasar nan.
A cewarsa, manufofin APC sun jefa yawancin ’yan Najeriya cikin wahala da ƙunci, tare da raunana rayuwar al’umma da tattalin arzikin ƙasa.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/komai-runtsi-ba-zan-bar-pdp-bahar-yanzu-ni-ne-babban-dan-adawa-a-najeriya-atiku/
Duk da haka, Atiku Abubakar ya jaddada cewa yana nan tsaye daram wajen haɗa kai da masu kishin ƙasa masu irin wannan hangen nesa domin dawo da kyakkyawan shugabanci, tare da gabatar wa ’yan Najeriya sahihin madadin da zai kawo sauƙi ga rayuwa, ya farfaɗo da fata, tare da tabbatar da ci gaba mai ɗorewa a ƙasar nan.

