Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun yi awon gaba da ɗan rajin kare haƙƙin bil’adama kuma ɗan siyasa a Najeriya, Omoyele Sowore, a wani gidan abinci da ke Jihar Ekiti.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a gidan abinci mai suna Tawakalitu Restaurants and Catering Services da ke Ado-Ekiti, inda maharan suka kutsa cikin wurin tare da lalata wasu kayayyaki da motoci.
Sowore, wanda yake takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 a ƙarƙashin jam’iyyar African Action Congress (AAC), ya sanar da faruwar lamarin ta shafukansa na sada zumunta.
Sai dai har zuwa lokacin da aka wallafa rahotannin, rundunar ’yan sandan jihar Ekiti ba ta tabbatar da sace shi ba, kuma ba a san inda yake ba.

