Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, zai bar Abuja a ranar Alhamis zuwa birnin Makka da ke ƙasar Saudiyya, domin gudanar da ibadar Umrah da kuma yi wa Najeriya addu’ar zaman lafiya, haɗin kai da ci gaba.
Wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Laraba, 28 ga Oktoba, 2026, ta bayyana cewa ziyarar za ta bai wa shugaban ƙasar damar yin ibada da kuma neman shiriya da albarkar Allah ga Najeriya da al’ummarta.
Sanarwar ta ce yayin zamansa a Makka, Tinubu zai gudanar da ibadun Umrah tare da yin addu’o’in samun zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaba mai ɗorewa a ƙasar.
Kafin tashinsa, shugaban ƙasar ya ƙaddamar da wasu kayan aiki da rundunar sojin saman Najeriya ta saya domin inganta ayyukanta.
Za a gudanar da bikin ƙaddamar da kayan aikin ne a sashen jiragen shugaban ƙasa na filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.
Ana sa ran Tinubu zai dawo Najeriya mako mai zuwa, bayan kammala ibadar Umarah.

