Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, tunda fari ya buƙaci fadar shugaban ƙasa ta riƙa wallafa hotuna da bidiyoyi masu ɗauke da kwanan wata domin tabbatar da cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana Saudiyya domin gudanar da ibadar Umrah.
Bayan kalaman Atiku kan tafiyar Tinubu umara, wasu daga cikin yan Najeriya sun goyi bayan kalaman na Atiku.
Atiku ya bayyana hakan ne yayin da yake nuna buƙatar samun ƙarin bayani kan halin da tafiyar shugaban ƙasar take ciki, tare da neman fadar shugaban ƙasa ta bayyana cikakken jadawalin ziyarar.
Haka kuma, ya yi wasu tambayoyi kan makasudin tafiyar, inda ya nuna shakku game da wasu bayanai da suka shafi ziyarar. Sai dai har yanzu waɗannan tambayoyi da zarge-zargen nasa ba su zama hujjar cewa shugaban ƙasar ya sauya inda ya nufa ba.
Saidai Fadar shugaban kasa bata nuna Naam ko akasin haka ga bukatar ta Atiku ba, amma dai an hango shafin Haramain sun wallafa hotunan Tinubu yana dawafi a Ka’aba lokacin sauke ibadar ta umara.

