Shugaban ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya (NLC), Joe Ajaero, ya jaddada cewa ƙungiyarsa na da ikon tattaunawa da bangaren gwamnati da suka shafi ma’aikata ita kaɗai, ba tare da sai an haɗa da ƙungiyar TUC ba.
Ajaero ya bayyana cewa TUC za ta iya shiga tattaunawar tare da NLC, amma ba za ta iya gudanar da irin wannan tattaunawa ita kaɗai ba, bisa ƙa’idar wakilcin mafi yawan ma’aikata ta ƙungiyar ƙwadago ta duniya (ILO).
Ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, yayin wata hira da gidan talabijin na Channels a cikin shirin The Morning Brief, a daidai lokacin da ake samun saɓani tsakanin ƙungiyoyin ƙwadago biyu kan alawus ɗin sufuri na naira dubu saba’in da gwamnatin tarayya ta amince za ta riƙa bai wa ma’aikata na tsawon watanni shida.
Shugaban NLC ya ƙara da cewa, bisa ƙa’idar ILO, ƙungiyarsa na da damar gudanar da tattaunawa ita kaɗai, yayin da TUC za ta iya shiga tattaunawar ne tare da ita.
Ajaero ya kuma ce idan TUC na da wasu shawarwari da suka shafi tattaunawa da ILO, ya kamata ta miƙa su ga NLC domin gabatar da su ga ƙungiyar ta duniya.
Ya bayyana cewa a baya TUC ta taɓa miƙa nata shawarwarin kai tsaye kafin wani taron ILO, amma aka mayar da su, inda shi ma ya ce sai da ya yi rubutu a kansu.

