Gwamnatocin Katsina da Plateau sun rufe dukkan makarantun gwamnati nan take, sakamakon ƙara ta’azzarar matsalar tsaro a jihohin.
A Katsina, kwamishinan ilimi na firamare da sakandare, Yusuf Jibia, ya bayyana cewa an dauki matakin ne domin kare rayukan dalibai da malamai yayin da gwamnati ke sake duba tsaron makarantu musamman a yankunan da ke da hadari.
Ya ce rufe makarantun zai kasance na ɗan lokaci ne har sai an kammala sabon tsarin tsaro da ake aiki akai.
Wani Labarin: RASHIN TSARO:An rufe makarantu a wasu kananan hukumomi na jihar Kwara
A jihar Plateau kuwa, hukumar kula da ilimi tun daga tushe ato SUBEB ta sanar da rufe makarantun kwana na furamare da Karamar sakandire daga gobe Asabar 22 ga Nuwamba, 2025.
Sanarwar tace a makarantu jeka ka dawo za’a rufe daga Litinin 24 ga Nuwamba, 2025. Hukumar ta ce matakin na da nufin taka-tsantsan ne domin kauce wa duk wata barazana da ka iya tasowa.
Gwamnatocin biyu sun bayyana cewa rufe makarantun na da nasaba da karuwar sace-sacen dalibai a wasu jihohin arewa, musamman a Kebbi da Neja, lamarin da ya sanya gwamnatoci makwabta kara shirin kare rayuka.
Wani Labarin: Manyan Janar na Soja sama da 50 za su yi Ritayar dole bayan Sauyin Shugabannin tsaro da Tinubu ya yi
Hukumomin ilimi sun bukaci shugabannin makarantu, hukumomin karamar hukuma da iyaye su tabbatar da bin umarnin, tare da kasancewa cikin shiri da lura da duk wani abu da zai iya jawo barazana.
TST Hausa ta rawaito cewa tunda farko gwamnatin jihar Kwara ce ta fara rufe makarantun gwamnatin jihar a wasu kananan hukumomi guda hudu saboda kara ta’azzarar matsalar tsaro

