Rahotanni daga jaridar Leadership Weekend sun bayyana cewa sabbin nadin shugabannin rundunonin tsaro da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi zai haifar da ritayar dole ga manyan hafsoshi fiye da hamsin, domin bin tsarin soja na ritayar wadanda suka fi sabbin shugabanni shekaru a aiki.
Sabbin shugabannin da aka nada duk ’yan Aji na 40 ne na makarantar horas da sojojin Najeriya kuma za su maye gurbin tsofaffin shugabanni ’yan Kwas na 39, ciki har da sabon Babban Hafsan Tsaro, Janar Olufemi Oluyede.
Da wannan sauyi, an bayyana cewa hafsoshi daga yan Aji na 39 da wasu daga daga Aji na 40 za su bar aiki, domin ba a yarda da hafsin soja ya ci gaba da zama a karkashin wanda yake ƙasa da shi ba a tsarin rundunar.
Rahotanni sun nuna cewa har yanzu wasu daga cikin yan Aji na 39 suna rike da manyan mukamai a hedikwatar rundunonin tsaro da kuma a matsayin shugabannin cibiyoyin horarwa na hadin gwiwa.
Majiyoyin soja sun tabbatar da cewa fiye da hafsoshi 50 ne ake sa ran za su yi ritaya domin ba sabbin shugabanni damar gudanar da ayyukansu cikin cikakken iko da tafiyar da rundunar yadda ya dace.
TST Hausa ta rawaito cewa a ranar juma,a ne shugaba Bola Tinubu ya sauke manyan hafsoshin sojojin Najeriya inda yace sauyin yana da alaka da tabbatar da tsaron kasa

