Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da sabbin motocin da za’a rika amfani da su domin ƙarfafa bibiyar yadda ake gudanar da shirin ciyar da al’umma a watan Ramadan a faɗin ƙananan hukumomi 44 na jihar.
Kwamishinan addinai na jihar Kano kuma Shugaban kwamatin kula da ciyarwa a watan Ramadan Sheikh Ahamad Tijjani Awwal da Sakatarensa Hon. Akibu Sani Murtala sune suka jagoranci kaddamar da motocin a gidan gwamnatin jiha.
Kwamishinan yace matakin na da nufin tabbatar da cewa ana aiwatar da shirin cikin tsari, da gaskiya da adalci, tare da tabbatar da cewa tallafin abincin na kaiwa ga waɗanda aka tanada domin su amfana da shi ba tare da tangarda ba.
Gwamnatin ta ce ƙaddamar da motocin wani ɓangare ne na sabbin matakan da aka ɗauka domin inganta tsarin shirin Ramadan, musamman a daidai lokacin da ake fuskantar ƙalubalen tsadar rayuwa.
Sheikh Tijjani ya kuma bayyana gamsuwarsa kan samar da motocin da kuma yadda ya gansu.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/ramadan-gwamnatin-kano-ta-fitar-da-shawarwari-kan-kula-da-lafiya-da-nauin-abincin-da-ya-kamata-a-ci/
TST Hausa ta rawaito cewa tunda farko Gwamnatin Kano ta ware naira miliyan dubu 4 da rabi domin ciyarwa a watan na Azumi.
Gwamnatin ta ce Shirin ciyar da abinci a watan Ramadan na daga cikin manyan shirye-shiryen jin ƙai da Gwamnatin Jihar Kano ke aiwatarwa duk shekara domin tallafa wa marasa ƙarfi, da rage radadin rayuwa a lokacin azumi.
Ana sa ran motocin za su fara aiki nan take domin tabbatar da cewa shirin ya gudana cikin nasara da kwanciyar hankali a dukkanin sassan jihar.

