A cikin wata sanarwa da ya wallafa bayan kammala ziyarar tasa zuwa Saudiyya, Tinubu ya ce addu’o’in da ya yi sun mayar da hankali ne kan samun zaman lafiya, haɗin kai, kwanciyar hankali da ci gaban Najeriya.
Ya kuma bayyana cewa ya roƙi Allah Ya ba shi hikima da ƙarfin guiwa domin ci gaba da sauke nauyin jagorancin al’ummar Najeriya.
Shugaban ƙasar ya gode wa Sarkin Saudiyya, Salman bin Abdulaziz Al Saud, da Yarima Mai Jiran Gado, Mohammed bin Salman, bisa damar da suka ba shi tare da tawagarsa ta shiga cikin ɗakin Ka’aba domin gudanar da addu’a.
Tinubu ya bayyana damar shiga Ka’aba a matsayin wata babbar ni’ima da tarihi da ba zai manta da ita ba.
A cewarsa, mulki amanar Allah ne, wanda yake bayarwa ga wanda Ya so, kuma yake karɓewa a duk lokacin da Ya so.

