Ma’aikatar harkokin kula da addini a kasar Saudiyya ta sanar da wasu sabbin matakai kan yadda za a gudanar da lokutan sallah a masallatan Harami na makka da Madina da ke karɓar alhazai a yayin aikin Hajjin shekarar 2026.
Ma’aikatar harkokin addinin ta ce an ɗauki matakin ne domin rage cunkoso, sauƙaƙa zirga-zirgar alhazai, da kuma taimaka musu wajen gudanar da ibadu cikin natsuwa musamman a lokutan da ake samun taruwar jama’a masu yawa.
Sabbin tsare-tsaren sun nuna cewa za a rika ɗaukar mintuna 15 tsakanin kiran sallar Asubah da iqama, yayin da Azahar da La’asar da Isha’i za su kasance da tazarar mintuna 10.
Ita kuwa sallar Magariba za ta kasance da tazarar mintuna biyar kacal tsakanin kiran sallah da Iqama.
Haka kuma, hukumomin Saudiyya sun bayyana cewa an umurci limamai da su rage tsawon hudubar Juma’a, inda aka kayyade huduba tare da sallah gaba ɗaya zuwa kusan mintuna 15, musamman saboda tsananin zafi da kuma yawaitar alhazai a lokacin Hajji.
Rahotanni sun nuna cewa matakin na daga cikin manyan shirye-shiryen da Saudiyya ke aiwatarwa domin inganta kula da mahajjata daga sassa daban-daban na duniya, tare da tabbatar da gudanar da ibadu cikin tsari, sauƙi da kariya ga lafiyar alhazai

