Kwamishinan Matasa da Wasanni na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayyana cewa gwamnatin jihar za ta yi ƙoƙarin taimaka wa wasu daga cikin magoya bayan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na Barcelona da Real Madrid wajen samun takardun izinin shiga ƙasashen waje domin kallon wasannin ƙungiyoyin biyu kai tsaye a filayensu.
Kwamared Waiya ya bayyana hakan ne jim kaɗan bayan wani zama na musamman da ya yi da wakilan ƙungiyoyin magoya bayan Barcelona da Real Madrid a jihar Kano.
Ya ce, ganin irin ƙwazo da haɗin kan da magoya bayan ƙungiyoyin biyu ke nunawa, gwamnatin jihar za ta yi ƙoƙarin ganin wasu daga cikinsu sun samu damar ziyartar filayen wasannin ƙungiyoyin biyu domin kallon wasanni kai tsaye.

