Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya amince da ware naira biliyan 89.2 domin gina titin Ring Road mai tsawon kilomita 47 a Bichi, Jihar Kano, wanda zai ƙunshi gadar sama (Flyover).
Ministan Ayyuka na Ƙasa, Sanata Dave Umahi, ne ya bayyana hakan yayin da yake yi wa manema labarai bayani kan sakamakon taron Majalisar Zartarwa ta Ƙasa (FEC) da aka gudanar a ranar Laraba, 28 ga Oktoba, 2026, a Abuja.
Amincewar na daga cikin ayyukan tituna da gwamnatin tarayya ta amince da su domin inganta sufuri, sauƙaƙa zirga-zirga da kuma bunƙasa harkokin kasuwanci.
A wani rubutu da mai taimakawa dan Majalisar Wakilai mai wakilitar Bichi Abubakar Aminu Ibrahim ya wallafa ya shaida cewa mutanan Bichi sunyi godiya ga shugaban kasa Bola Tinubu.
Ana sa ran titin zai inganta haɗin kai tsakanin al’ummomi tare da sauƙaƙa jigilar mutane da kayayyaki a yankin Bichi da kewaye.

