Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana cewa a halin yanzu Najeriya ba ta da wani mutum da ke dauke da cutar Ebola, bayan dauke matar da aka tabbatar tana dauke da cutar tare da mijinta zuwa ƙasar Switzerland domin ci gaba da kula da su.
Daraktan hukumar WHO mai kula da yankin Afirka, Farfesa Mohamed Janabi, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin, inda ya ce an kwashe ma’auratan ne ta jirgin musamman na kula da marasa lafiya.
Ya bayyana cewa matar, wadda ’yar ƙasar Switzerland ce, ta samu kulawa daga jami’an lafiya na Najeriya, waɗanda suka taimaka wajen daidaita yanayinta bayan ta shiga mawuyacin halin cutar.
Farfesa Janabi ya yabawa Gwamnatin Tarayya, ma’aikatan lafiya da sauran jami’an da suka taka rawa wajen kula da mara lafiyar, yana mai cewa nasarar da aka samu ta nuna ƙwarewar jami’an lafiya na Afirka.
Duk da haka, ya jaddada muhimmancin ci gaba da sanya ido domin hana sake yaɗuwar cutar.
Ya ce hukumomin lafiya na Najeriya za su ci gaba da sa ido kan mutane 52 da suka yi mu’amala da matar, yayin da hukumomin Switzerland za su kula da ita tare da sa ido kan mijinta, wanda shi ma aka sanya cikin jerin waɗanda aka yi hulɗa da mara lafiyar.

