Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar SDP, Prince Adewole Adebayo, ya yi gargaɗin da kada a fake da barkewar cutar Ebola a dakatar da yaƙin neman zaɓe ko a ɗage babban zaɓen 2027.
Adebayo ya yi gargadin ne yana mai cewa samun mutum guda da aka tabbatar yana ɗauke da cutar bai isa a bayyana barkewar annoba a ƙasar baki ɗaya ba, yana mai cewa za a iya kare lafiyar jama’a ba tare da kawo cikas ga harkokin zaɓe ba.
Ɗan takarar ya bayyana hakan ne a wani liyafar cin abinci da shugabannin kwamitin yaƙin neman zaɓensa suka shirya a Abuja.
Ya ce Najeriya ta taɓa fuskantar bullar Ebola a shekarar 2014, a lokacin mulkin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, inda aka shawo kan lamarin ta hanyar ɗaukar matakan da suka dace kuma hakan bai hana, zaben 2015 ba.
Adebayo ya kuma buƙaci hukumomin gwamnati da su tabbatar da gaskiya da bayyana bayanai game da halin da ake ciki, tare da kira ga ’yan Najeriya da su ci gaba da bin shawarwarin hukumomin lafiya.
A nasa ɓangaren, Ministan Lafiya da Walwalar Jama’a, Farfesa Muhammad Ali Pate, ya bayyana cewa babu buƙatar gaggawar soke yaƙin neman zaɓe ko sauran manyan taruka a halin yanzu, sai dai gwamnati za ta yi la’akari da ɗaukar matakan takaita taruka idan yanayin cutar ya tsananta.
Adebayo ya ce jam’iyyarsa za ta ci gaba da wayar da kan jama’a tare da bin ƙa’idojin lafiya, yana mai cewa bai kamata a yi amfani da batun cutar wajen kawo cikas ga zaɓen 2027 ba.
Ya kuma bayyana cewa jam’iyyar SDP ta fassara kundin manufofinta zuwa harsuna daban-daban, ciki har da Hausa, Igbo da Yarbanci, domin bai wa ’yan Najeriya damar fahimtar manufofinta kafin zaɓen.
Ya ce kundin ya mayar da hankali kan tsaro da walwalar jama’a, waɗanda ya bayyana a matsayin manyan nauyin da ke kan kowace gwamnati.

