Limamin Masallacin Usman Bin Affan da ke Unguwar Gadon Kaya a Kano, Dr. Abdallah Usman Gadon Kaya, ya yi gargaɗi ga al’ummar Musulmi kan haɗa Allah da wani wajen bauta, yana mai cewa hakan na iya jawo wa mutum hasara a duniya da lahira.
Malamin ya bayyana hakan ne a cikin hudubar Juma’a, inda ya yi bayani kan muhimmancin bautar Allah shi kaɗai ba tare da haɗa shi da wani ba, tare da bayyana illolin shirka ga rayuwar Musulmi.
Dr. Abdallah Gadon Kaya ya ce dukkan annabawan da Allah ya aiko sun haɗu a kan kira guda, wato bautar Allah shi kaɗai da kuma nisantar duk wani nau’in shirka.
Ya bayyana cewa a wannan zamani, ana samun yaɗuwar wasu ayyuka da suka saɓa wa tauhidi, ciki har da bokanci da wasu nau’o’in ayyukan da ke iya kai mutum ga shirka.
Malamin ya ba da misalan irin waɗannan ayyuka da suka haɗa da neman biyan buƙata ta hanyar bokaye, da kuma wasu ayyukan da suka shafi kaburbura da ɗaukaka wasu mutane ta hanyar da ta saɓa wa koyarwar Musulunci.
Haka kuma, Dr. Abdallah Gadon Kaya ya yi gargaɗi kan yadda wasu ’yan siyasa ke nuna halaye ko furucin da ke iya nuna raunin imani da ƙaddarar Allah, musamman dangane da batun mulki da shugabanci.
Ya jaddada muhimmancin tabbatar da tauhidi a cikin dukkan al’amuran rayuwa, yana mai kira ga Musulmi da su riƙa komawa ga koyarwar Alƙur’ani da Sunnah wajen gudanar da ibadunsu da sauran harkokinsu na yau da kullum.
Malamin ya kuma yi kira ga al’umma da su ƙara fahimtar koyarwar addininsu, tare da nisantar duk wani aiki ko akida da ka iya gurɓata tauhidi, domin samun tsira a duniya da lahira.

