Limamin Masallacin Usman Bin Affan da ke Gadon Kaya, Dr. Abdallah Gadon Kaya, ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su kiyaye dokokin Allah, yana mai cewa duk wanda ya kiyaye dokokinsa, Allah zai kiyaye shi tare da shiryar da shi zuwa ga abin da ya dace.
Dr. Abdallah ya bayyana hakan ne a hudubar Juma’a da ya gabatar a Masallacin Usman Bin Affan da ke Gadon Kaya, inda ya ja hankalin jama’a kan bukatar nisantar aikata laifuka da zunubai, ciki har da zina, luwaɗi, caca, shan giya da sauran abubuwan da Shari’ar Musulunci ta haramta.
Ya kuma yi kira ga jama’a da su rika kiyaye iyalansu da tarbiyyarsu, tare da tsayawa kan koyarwar addini.
Limamin ya kuma bukaci jama’a da su rika ƙidaya ni’imomin Allah da Ya yi musu, su gode Masa, sannan su yi amfani da waɗannan ni’imomi wajen aikata abin da Ya yarda da shi.
Ya ce mutum na bukatar ya riƙa duba halayensa da ayyukansa domin sanin ko yana bin dokokin Allah yadda ya kamata.
Dr. Abdallah ya ƙara jan hankalin jama’a kan muhimmancin kiyaye sallah, yana mai cewa rashin yin sallah a lokacinta na daga cikin gazawar mutum wajen kiyaye dokokin Allah.
Yace da yawan mutane musamman magidanta sun daina sallah amma ba kowa ne zai sani ba sai iyalan wanda abin ya shafa ko wanda yake da alaka da abin ba tare da wani dalili ba.
Ya yi kira ga Musulmi da kada su yi sakaci da sallah, domin ita ce ginshiƙin ibada kuma wajibi ne a kiyaye lokutanta.

