Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da cewa ta kammala tantance kuɗin aikin Hajjin bana, inda ta tsaida kuɗin zuwa Naira miliyan bakwai (₦7,000,000) ga kowane mahajjaci.
Hukumar a wata sanarwa da maimagana da yawunta Sulaiman A Dederi ya fitar yace an kuma tabbatar da cewa 25 ga Agusta, 2026 ce ranar ƙarshe da aka sanya domin kammala rijistar masu niyyar zuwa aikin Hajjin.
Daraktan-Janar na Hukumar, Alhaji Abubakar Ibrahim Matawalle, ne ya bayyana hakan a yau yayin taron manema labarai da ya gudanar a ɗakin taron hukumar da ke Kano.
Ya ce bayan kammala nazari kan abubuwan da suka shafi gudanar da aikin Hajjin, an tsaida kuɗin zuwa ₦7,000,000 kacal ga kowane mahajjaci.
Daraktan-Janar ɗin ya kuma yi gargaɗin cewa ba za a ƙara wa’adin rijistar ba bayan ranar da aka sanya, inda ya buƙaci duk masu niyyar zuwa Hajjin da ba su kai fasfo ɗin ƙasa da ƙasa ba, su gaggauta miƙa shi kafin cikar wa’adin.
Ya ce bin wannan wa’adi na da matuƙar muhimmanci domin ba wa hukumar damar kammala shirye-shiryen da suka dace kafin fara aikin Hajjin.
Alhaji Abubakar Matawalle ya buƙaci masu niyyar zuwa Hajjin da sauran masu ruwa da tsaki da su kula da wannan sanarwa tare da bin umarnin hukumar domin kauce wa duk wani cikas da ka iya tasowa.
Hukumar ta ce za ta ci gaba da ƙoƙarin samar da ingantaccen tsari da kuma ayyuka masu sauƙaƙa wa alhazan Jihar Kano gudanar da ibadar Hajji cikin kwanciyar hankali da nasara.
TST Hausa ta rawaito cewa a baya Hukumar Alhazan ta nemi maniyata su ajiye naira Miliyan 8 a matsayin kudin ajiya kafin yanke hukunci kan farashin karshe.

