Shugabar Ƙaramar Hukumar Tudun Wada kuma shugabar ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomin Jihar Kano (ALGON), Hajiya Sa’adatu Yusha’u Soja, ta sayi tabarmi da butoci domin rabawa a wasu masallatai a matsayin Sadakatul-Jariya ga marigayi fitaccen mawakin siyasa, Muhammad Buhari, wanda aka fi sani da Kosan Waka.
Hajiya Sa’adatu ta bayyana hakan ne yayin addu’ar cikar kwanaki bakwai da rasuwar marigayin, inda ta miƙa kayan ta hannun mataimakin shugaban ƙungiyar mawallafan Abba Gida-Gida, Alhaji Auwal Lamari Sharada.
Ta bayyana matakin a matsayin wata hanya ta tunawa da marigayin tare da neman lada da rahama a gare shi.
Hajiya Sa’adatu ta kuma yabawa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, bisa irin rawar da ya taka wajen tabbatar da cewa an gudanar da jana’izar marigayin cikin tsari ba tare da wata matsala ba.
Ta sake mika saƙon ta’aziyyarta ga iyalan marigayin, ’yan uwa, abokan arziki da kuma ƙungiyar mawallafan Abba Gida-Gida bisa wannan babban rashi.
Ta kuma roƙi Allah Ya jiƙan marigayin, Ya gafarta masa, Ya sanya shi cikin rahamarSa, sannan Ya ba iyalansa da sauran waɗanda suka rasa shi haƙurin jure wannan rashi.

