Bayan watanni da fuskantar ɗaya daga cikin mafi munin ibtila’in da ya girgiza Jihar Kano, Haruna Bashir, wanda ya rasa matarsa Fatima Abubakar da ‘ya’yansu shida a wani mummunan hari da ya faru a unguwar Chiranchi (Dorayi), ya sake fara sabon babi na rayuwarsa bayan shiga cikin Shirin Auren Gata da Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya shirya.
Haruna Bashir na daga cikin angwaye 1,500 da aka daura wa aure a karkashin shirin Auren Gata da gwamnatin jihar ta gudanar domin tallafa wa matasa wajen gina ingantattun iyalai da rage kalubalen rashin aure.
Bayan faruwar lamarin Gwamna Abba yaci alwashin sake daurawa malam Haruna wani auren bayan mika masa gida da akayi da kaishi aikin Hajji.
Za a iya tunawa cewa a ranar 17 ga Janairun 2026, wasu mahara sun kutsa cikin gidan Haruna Bashir da ke unguwar Chiranchi, inda suka kashe matarsa Fatima Abubakar mai shekaru 35 da kuma ‘ya’yansu shida. Lamarin ya jefa Kano da Najeriya baki ɗaya cikin alhini, inda jama’a suka yi ta kira ga hukumomin tsaro da su tabbatar da an gano tare da hukunta masu hannu a wannan mummunan ta’asa.
Bayan gudanar da bincike, Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta cafke wasu da ake zargi da hannu a kisan, ciki har da Umar Auwalu, wanda ake zargin ɗan wa ne ga marigayiya Fatima Abubakar. ‘Yan sanda sun bayyana cewa bincikensu ya nuna shi ne ya shirya harin tare da wasu mutane.
Daga bisani, an gurfanar da waɗanda ake tuhuma a gaban kotu domin amsa tuhume-tuhume da suka haɗa da haɗa baki, kisan kai da sauran laifukan da suka shafi wannan al’amari.
Shari’ar ta fara gudana, inda kotu ta bayar da umarnin ci gaba da tsare waɗanda ake tuhuma tare da ɗage sauraron karar zuwa wasu ranaku domin ci gaba da gabatar da hujjoji da kuma sauraron shaidu. Har zuwa yanzu, ana ci gaba da sauraron shari’ar a kotu, kuma ba a yanke hukunci na ƙarshe ba.
Yanzu, bayan watanni na jimami da jarrabawa, Haruna Bashir ya sake samun damar fara sabuwar rayuwa ta hanyar shiga Shirin Auren Gata.
Lamarin ya ja hankalin jama’a, inda da dama ke bayyana cewa hakan wata alama ce ta ƙoƙarin ci gaba da rayuwa duk da irin babban rashi da ya fuskanta, tare da fatan Allah Ya ba shi zaman lafiya, Ya kuma jiƙan matarsa da ‘ya’yansa da rahama.

