Gwamnatin kasar Saudiyya ta dauki wani sabon mataki na inganta jin dadin alhazai yayin aikin Hajjin shekarar 2026, inda ta maye gurbin tsofaffin na’urorin sanyaya waje guda 45,600 da sabbin na’urori masu inganci a tantunan Mina.
Rahotanni sun ce an shigo da sabbin na’urorin ne daga kasar Australia, domin taimakawa wajen rage radadin zafin rana da alhazai ke fuskanta a lokacin gudanar da aikin Hajji.
Matakin na zuwa ne yayin da mahukuntan Saudiyya ke ci gaba da fadada ayyukan more rayuwa da inganta wuraren ibada domin samar da sauki da kariya ga miliyoyin musulman da ke zuwa kasa mai tsarki daga sassa daban-daban na duniya.
Mina, wacce ke kusa da birnin Makkah, na daga cikin wuraren da alhazai ke kwana yayin gudanar da muhimman ibadun Hajji.
A duk shekara, miliyoyin mahajjata kan taru a dubban tantunan da aka tanada domin sauka da hutawa gabanin Arfa da Jifan shaidan.
Masana na ganin cewa girke wadannan sabbin na’urorin sanyaya iska zai taimaka sosai wajen rage tasirin tsananin zafi, musamman ganin yadda yanayin zafi ke karuwa a lokacin bazara a kasar Saudiyya.
Haka kuma, ana kallon wannan shiri a matsayin wani bangare na manufofin Saudiyya na kara inganta aikin Hajji tare da tabbatar da jin dadi da lafiyar alhazai yayin gudanar da ibadunsu.

