Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane takwas a ƙauyen Garin Idi da ke Ƙaramar Hukumar Sabon Birni a Jihar Sakkwato, ciki har da wasu da ake zargin ’yan uwan Mataimakin Gwamnan jihar Dr. Mannir Muhammad Dan Iya ne.
Rahotanni sun nuna cewa harin ya faru ne da misalin ƙarfe 1 na daren ranar Alhamis, inda maharan suka shiga ƙauyen a kan babura, tare da yin harbi kan mai uwa da wabi, lamarin da ya tilasta mazauna yankin tserewa domin neman tsira.
Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa maharan sun yi ta kai farmaki na kusan awa biyu ba tare da wani tsayawa ba, kafin daga bisani su yi awon gaba da mutanen zuwa wani wuri da ba a sani ba.
Ya ƙara da cewa babu wani taimakon gaggawa daga jami’an tsaro a lokacin da lamarin ke faruwa, wanda hakan ya ƙara jefa al’umma cikin fargaba.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a samu cikakken bayani daga hukumomin tsaro ba game da matakan da ake ɗauka domin ceto waɗanda aka yi garkuwa da su.

