Babban shafin tallata tafiyar Kwankwasiyya karkashin Jagorancin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a Facebook wato Kwankwasiyya Reporters ya sanar da sauya sunan shafinsa zuwa Gida Gida Reporters, a wani mataki da ya ce an ɗauka domin ƙarfafa rawar da shafin yake takawa wajen wayar da kan al’ummar Jihar Kano kan harkokin mulki da ayyukan gwamnatin Abba Kabir Yusuf.
A cewar sanarwar da wakilin shafin Muhammad M. Alasan, ya fitar ga manema labarai na gidan Gwamnatin Kano, sauyin sunan na da nufin mayar da hankali kan yaɗa bayanai da rahotanni game da tsare-tsare, da manufofi da ayyuka masu amfani ga jama’a da gwamnatin Jihar Kano ke aiwatarwa ƙarƙashin jagorancin Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/ina-tuna-doguwar-tafiyar-siyasa-da-rikon-amana-tsakaninmu-kwankwaso-ya-taya-gwamna-yusuf-murnar-zagayowar-ranar-haihuwa
TST Hausa ta rawaito cewa an kirkiri shafin ne tun a shekarar 2016 domin tallata akidar tafiyar tsohon gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso karkashin Jagorancin shugaban karamar hukumar Kumbotso Ghali Basaf.
Shafin na Kwankwasiyya Reporters da aka Sauyawa suna yana da mabiya dubu 720 a yanzu haka tun bayan samar da shi.
Sanarwar ta kuma yi tsokaci kan rade-radin cewa an sauyawa shafin suna ne domin juyawa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso baya,inda Muhammad Alassan yace har yanzu shafin na alfahari da Jagoran na Kwankwasiyya kuma suna kallonsa a matsayin jagora kuma uba.
Muhammad ya kuma shaidawa TST Hausa cewa sun mika batun sauya sunan, ga hukumomin Facebook inda suke jiran amincewa.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/gwamna-yusuf-na-da-yancin-barin-nnpp-zuwa-apc-kamar-yadda-kwankwaso-ya-bar-pdp-zuwa-nnpp-shekarau/
Sabon shafin na Gida Gida Reporters ya jaddada cewa za su cigaba da bin ka’idojin aikin jarida na gabatar da sahihai da nagartattun labarai na gaskiya, tare da kauce wa yaɗa jita-jita, sai dai rahoto kan duk wani ci gaba da ya samu daga tushe ingantacce.
Sabon shafin ya ƙara da cewa zai cigaba da aiki tukuru domin tabbatar da cewa al’ummar Kano sun samu sahihin bayani game da harkokin siyasa da ayyukan gwamnati, a kowanne lokaci da canji ya faru.

